’Yan kasuwar Rimi a Kano sun koka kan ruguje rumfunansu

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Wasu ‘yan kasuwa da ke kasuwar Rimi cikin ƙaramar hukumar birnin Kano sun koka kan yadda suka wayi garin Talata da labari mara daɗi na cewa jami’an tsaro da wasu da suka ce lauyoyi ne sun bayyana da asubahi Talata, inda suka rushe rumfuna 18 na wani sashi na kasuwar Rimi cikin birnin Kano.

Malam Iliyasu Muhammad mai sana’ar siyar da mai a kasuwar ya ce suna zaune a wannan wuri ne tun kimanin shekaru 20 da suka wuce a matsayin sashin rumfunan temfurare wato na wucin gadi, wanda aka basu tun lokacin da aka gina jan bulo, saboda su basu samu ba amma aka ce ga wannan, ƙaramar hukumar birnin Kano ta basu takardar izinin zama a wannan guri amma aka wayi ɓari da asubahi aka ce ga wasu jami’ai nan sun zo rushe rumfuna wanda kuma hakan ce ta kasance na rushe rumfuna a kasuwar Rimi a Kano.

Har ila yau , Malam Iliyasu ya ce dama shekara wajen bakwai suna shari’a da wani mai gidan wanka wanda ba ya son zamansu a wurin, kuma har yanzu ba su san na waye ba, sai dai sun tashi tsaye wajen gano shi ta hanyar hukuma da ta dace, domin da suka tambaya sai aka ce kotu ce ta bada umarnin rushe rumfunan su. 

Haka shi ma Alhaji Sani Mai Turare ya ce shi ne wakilin ‘yan kasuwa da ke bin wannan shari’a a kotu, Miller Road mai lamba 15.

Sai dai kuma kan wannan lamari na rushe rumfuna da aka ce kotu ta yi wakikin Manhaja ya tuntuɓi Baba Jibo Ibrahim kakakin kotun jihar Kano ya ce ba shakka wannan hukunci babar kotu ce ta yanke wannan hukunci na rushe rumfuna sakamakon filin wani ne da ya kai ƙara kan filin sa na gidan wanka. Shari’ar da ta kwashe fiye da shekara takwas ana yin ta sai wannan karon aka yanke hukunci.

Haka kuma wakilin Manhaja ya yi ƙoƙarin jin ta bakin hukumar kula da gine-gine ta jihar Kano kan wannan lamari amma abun ya ci tura.

A ƙarshe ɗaukacin ‘yan kasuwar sun koka kuma suna neman taimako daga gwamnan Kano da Sarkin Kano da sauran masu faɗa aji ka a kawo musu agaji na halin ni-‘ya-su sakamakon rushe waɗannan rumfuna da suke neman abinci a cikin su.