‘Yan Majalisar Zamfara sun zaɓi sabon shugaba

Daga BASHIR ISAH

‘Yan Majalisar Jihar Zamfara sun zaɓi Honorabul Bilyaminu Isma’il daga Ƙaramar Hukumar Zurmi a matsayin sabon Shugaban Majalisar ba tare da hamayya ba.

Kazalika, sun zaɓi Adamu Aliyu Birnin Magaji daga Ƙaramar Hukumar Gummi a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar.

Sun gudanar da zaɓen ne a ranar Talata a zauren majalisar da ke Gusau, babban birnin jihar.