’Yan mazaɓar Sanata Natasha a Kogi sun ɗauki haramar yi mata kiranye 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mazaɓar Kogi ta tsakiya sun fara ɗaukar matakan yi wa sanatar da ke wakiltarsu, Natasha Akpoti-Uduaghan, kiranye daga majalisar dattawan ƙasar nan a yayin da aka fara rattaɓa hannu a wasu unguwanni a mazaɓar.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito a ranar Laraba cewa a Lakoja an fara tattara sa-hannu a ƙananan a ƙananan hukumomi 5 da suka shiyyar da sanatar take wakilta.

Wasu daga cikin wuraren da suka fara sun haɗa da: ƙananan hukumomin Ajaokuta, Adaɓi, Okene, Lokoja, da Okehi inda aka ga mutane suna ba da sa-hannunsu da nufin yi wa sanatar kiranye.

A ɗaya daga cikin wuraren, Ihima da ke ƙaramar hukumar Okehi wanda shi ne mahaifar ita sanatar, Mrs Akpoti-Uduaghan, an ga mutane a dogon layi suna sa-hannu domin yi mata kiranye.

Abdullahi Usman, wani mazaunin Ihima, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa cewa, ya shiga jerin masu sa-hannun ne don raɗin kansa saboda rasa ƙarfin guiwarsa da ya yi a kan wakilcin Mrs Akpoti-Uduaghan.

“Kana gani ai ga layi nan. Mutane sun fito ne su nuna rashin gamsuwarsu da wakilcinta a zauren majalisar bayan abin da ya faru na rikicinta da shugaban majalisar.”

”Muna aika wa duniya saƙo ne cewa ba mu gamsu da wakilcinta ba. Abin da ta aikata abin kunya ne a wajenmu kuma a gaban duniya,” inji Usman.

A wani wuri a Ajaokuta, wata mata Hajia Rabi Mohammed ta ce, “muna so ta dawo gida ne saboda mu zaɓi wani daban mai mutunci.”

Shi ma Samuel Adamu, daga cikin garin Lokoja ya ce, an fara wannan abu na yi wa sanatar kiranye ne ranar Laraba kuma za a ɗauki kwanaki biyu ana a dukkan mazaɓu da ke ƙananan hukumomi 5.

“Muna da tabbacin cewa daga yanzu zuwa 21 ga watan Maris, za mu kammala tattara wannan sa-hannun tare da rubuta ƙorafi ga majalisar domin a sauke mana sanatar,” inji Adamu.

Sannan ya ƙara da cewa; “mun ɗauki wannan abu da muhimmanci. Mun yi ƙoƙarin magana da ita, amma ba mu yi nasarar ba,” yana mai nuna damuwar mazauna yankin.

A yayin da yake magana, Abdulrahman Badamasiuyi, shugaban jam’iyyar PDP, ya bayyana wannan yunƙuri da bigibagiro.

Mista Badamasiuyi ya buƙaci ‘yan asalin mazaɓar da su yi watsi da wannan abu da aka shirya na yi wa Mrs Akpoti-Uduaghan kiranye daga majalisar.

“Muna son majalisa da ‘yan Nijeriya da duniya su sani cewa muna tare da sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan dakatar da ita da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.”

“Ta cikin mutanen da muka yarda da su da jagorancinsu. Kuma ba wanda yake da ikon ƙwace mana zaɓin da dimokraɗiyya ta ba mu damar mu yi.”

“Don haka, muna sanar da majalisa da ‘yan Nijeriya da duniya cewa Akpoti-Uduaghan za ta ci gaba da riƙe muƙaminta na sanata har zuwa kakar zaɓe ta 2027,” ya bayyana.