’Yan Najeriya za su ba wa ɗan takarar Gwamnan New York gudunmawar Dala 33,000

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai ]an takarar gwamnan Newyork ta Amurka, Mista Eric Adams, zai samu tagomashin gwaggwaɓar gudunmowa har ta dala dubu talalin da uku ($33,000) daga ‘yan Najeriya mazauna ƙasar ta Amurka.

An ba da gudunmowar gare shi ne domin ya yi yakin zaɓen da za a yi a kakar zaɓe ta watan gobe wato Nuwambar shekarar nan da muke ciki ta 2021. 

Shugaban kwamitin cigaban ‘yan Najeriya  a can ƙasar, Mista Yinka Dansalami, ya bayyana cewa, su ‘yan Najeriya na ƙasar Amurka za suna sane da yadda harkokin siyasa suke tafiya sannan kuma suna ba da gudunmowa a lokacin da ya dace.  

Dansalami ya ƙara da cewa, a yanzu haka ma akwai kimanin Dala dubu 25 a ƙasa kuma suna nan suna ta fafutukar cikasa sauran kuɗaɗen da suke da burin haɗawa wato dala dubu talatin da uku.

Kuma su na addu’a tare da fatan ɗan takarar tasu ya samu nasara. Da ma ‘yan magana sun ce, ana yi da kai ya fi ba a yi da kai.