‘Yan Nijeriya miliyan 14 ne ke ta’ammali da miyagun ƙwayoyi – NDLEA

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA, ta ce kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 14 ne ake kiyasin su ke ta’ammali da kuma shaye-shayen miyagun ƙwayoyi masu illa.

Mataimakiyar Kwamanda ta NDLEA reshen Jihar Ondo, Yetunde Joyifous, ta bayyana hakan a wani taron wayar da kan jama’a game da illar shaye-shaye, wanda ƙungiyar matasan Oijefon ta shirya ga ɗaliban makarantun sakandare a ƙaramar hukumar Ile Oluji/Oke-Igbo, a ranar Laraba.

Misis. Joyifous ta ce yawancin ƙwayoyin da ake sha sun ƙunshi sinadarai masu ikon sauya tunanin masu amfani da su ta hanyar da ba ta dace ba.

A cewarta, hanya ɗaya tak da za a daƙile wannan matsala ita ce haɗa hannu da dukkan masu ruwa da tsaki a cikin al’umma domin yin aiki tare da hukumomi wajen yaƙi da wannan mummunan kasuwanci.