‘Yan Nijeriya miliyan 25 za su shiga matsalar ƙarancin abinci a 2023 – FAO

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), ta bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 25.3 za su fuskanci mummunan matsalar ƙarancin abinci a tsakanin watannin Yuni da Agustan 2023.

A cikin sanarwar da FAO ɗin ta fitar, ta ce idan tun da wuri ba a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki ba, to mutum miliyan 4.4 a Barno, Adamawa da Yobe za su rasa cin yau da na gobe.

Cikin rahoton da hukumar ta fitar na watan Oktoba 2022, FAO ta ce a yanzu haka mutum miliyan 17 na rayuwar cin abincin da kwata-kwata ba mai gina jiki ba ne.

Ta ce mutanen miliyan 17 su na rayuwar ‘ya-mu-samu-ya-mu-sa-bakin-mu’, ba tare da zaɓen abin da ya dace, ya kamata ko ya wajaba su riƙa ci ba.

Waɗanda ke cikin wannan mawuyacin hali a cewar FAO, sun haɗa da dukkan jama’ar da ke zaune a sansanonin gudun hijira da waɗanda su ka koma gidajen su daga gudun hijira a jihohi 26 da yankin Abuja. Rahoton ya ce waɗannan mutane su na rayuwa ne, amma babu tudun dafawa.

Rahoton ya ce aƙalla irin waɗannan mutanen su miliyan 3 su na zaune a Barno, Adamawa da Yobe.

A ƙoƙarin da ake yi domin tallafa wa manoman waɗannan jihohi, Gwamantin Norway ta sake danƙara wa hukumar FAO kuɗaɗe domin ta taimakon manoman jihohin Yobe, Adamawa da Barno, waɗanda ke fama da wannan matsananciyar rayuwa.

An yi tsari na tsawon shekaru uku, wanda za a tallafi gidaje 43,990, daidai da mutane 307,930 kenan.

Kashi 45 na waɗanda za a tallafa wa ɗin mata ne, waɗanda za a tallafa masu da kayan aikin noma kaitsaye, jarin dabbobi ko jarin kiwon dabbobi, kuma za a ba su risho wanda ba mai aiki da itace ba ne.

Jakadan Norway a Nijeriya, Knut Eiliv Lein ya bayyana cewa ƙasar sa ta sha alwashin ci gaba da bayar da tallafi ga yankunan da rikice-rikice da kashe-kashe su ka illata a Arewa maso Yamma.