Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kamfanin Kula da Raba Wutar Lantarki a Nijeriya, wato TCN, ya bayyana cewa, duk da ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi a baya-bayan nan, har yanzu farashin lantarki a Nijeriya ya fi sauƙi a kan wasu ƙasashe makwabta na Afirka.
Manajan Daraktan TCN, Sule Abdulaziz, ne ya bayyana hakan a wani shiri na Sunday Politics a gidan talbiji na Channels.
Ya ce, ‘yan Nijeriya na ƙara biyan kuɗin wutar lantarki saboda samar da wutar lantarki ba abu ne mai sauƙi ba, kuma ‘yan ƙasar da ke rukunin Band A a yanzu suna samun wutar lantarki ta sa’o’i 24, lamarin da wasu mazauna yankin ke neman irinsa.
“‘Yan Nijeriya na samun lantarki na sa’o’i 24 a kullum, sai dai waɗanda ke cikin Band A, suna samun sa’o’i 20 zuwa 22,” inji Abdulaziz.
“’Yan Nujeriya na ƙara biyan kuɗi saboda samar da wutar lantarki ba sauƙi. Ina iya ganin canjin farashi.
“A yanzu wutar lantarki ta yi tsada a Nijeriya, muna kuka da tsada amma duk da haka muna samunsa a farashi mai rahusa. Idan ka je wasu ƙasashen Afirka, ka je Nijar, ka je Burkina Faso, ka je Senegal, har yanzu, Nijeriya ta fi araha.”
Ya kuma baiwa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa ƙasar za ta iya samun daidaiton wutar lantarki cikin kasa da shekaru biyar, yana mai cewa an samu ci gaba sosai wajen samar da wutar lantarki a shekarar da ta gabata.
“Idan ka tambayi ‘yan Nijeriya, dukkansu sun san cewa an samu ci gaba a mulki kuma wannan cigaban zai ci gaba,” inji shi.
A ranar 3 ga Afrilu, 2024, Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta ƙara farashin wutar lantarki ga abokan hulɗar da ke jin dadin samar da wutar lantarki na awanni 20 a kullum. Abokan ciniki a cikin wannan rukunin an ce suna ƙarƙashin rukunin Band A.
An fara aiwatar da ƙarin kuɗin wutar lantarki sau huɗu ne a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke cigaba da kokawa kan raɗaɗim da ake samu na cire tallafin man fetur wanda ya sa farashin man fetur ya ninka sau biyar.