Yan Nijeriya za zu yi murna idan aka rushe zaɓen Tinubu – PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar PDP ta ce ‘yan Nijeriya za su fito kan tituna suna murna idan har aka soke ayyana Bola Tinubu a matsayin Shugaban Ƙasa.

Sai dai a martanin da ta mayar cikin gaggawa, jam’iyyar mai mulkin ƙasar ta ce PDP na rugujewa ne kawai, inda ta dage cewa Shugaba Tinubu na da hurumin ‘yan Nijeriya kuma zai yi aiki a kan haka kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Pedro Obaseki, Daraktan Dabaru da Bincike na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na PDP (PCC) wanda ya yi wa manema labarai jawabi gabanin hukuncin da Kotun Sauraron Qararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa (PEPT) za ta yanke, ya kuma bayyana qwarin gwiwar cewa PDP ta yi imani da ikon ɓangaren shari’a gabatar da hukunci na gaskiya wanda zai zama karɓaɓɓe ga ɓangarorin da abin ya shafa.

Ya kuma ƙara da cewa, saboda ƙwararan shaidun da ke hannunsu, alƙalan kotun za su jajirce wajen magance matsalolin da suka taso, inda ya ce martabar ƙasar nan na cikin haɗari, lamarin da ya ce alƙalan ba za su yi wasa ba.

Obaseki, wanda lauya ne, ya yi magana musamman game da koken da Ƙungiyar Allied Peoples Movement (APM) ta gabatar na neman a soke nasarar Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima a zaɓen 2023 kuma ya lura cewa “batun cancanta shine mabuɗin”.

Ya ce: “Har yanzu da sauran lokacin da za a iya samun wannan lokacin ne kawai ta hanyar koken Allied Peoples Movement a wannan zaɓen. Wannan ba ta kowace hanya ba zai dakatar da sauran shaidu masu tasowa ba. Muna nan lokacin zaɓe ya zo, muna nan lokacin da aka ayyana zaɓe, muna nan muna jiran masu son yin murna, ba su yi bikin ba.

“Wataƙila ka yi mamakin cewa nan da nan aka yanke hukuncin da bai tabbatar da zaɓen da aka ce an yi na Shugaban Ƙasa Tinubu ba, mutane za su fito kan tituna suna murna; gaskiya kenan.”

Da yake mayar da martani, Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Barista Felix Moka, ya ce: “PDP ko duk wanda ke tunanin za a soke zaven Shugaban Ƙasa Tinubu, hasashe ne kawai.

“Shugaban Ƙasa ya lashe zaven a fili cikin tsafta kuma ‘yan adawa ba su da wata shaida a kansa.”

A halin da ake ciki, babban alƙalin alƙalan Nijeriya, Mai shari’a Olukayoode Ariwoola, ya musanta cewa ya tattauna ta wayar tarho da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da daraktan ma’aikatan tsaron farin kaya Yusuf Bichi, kan ƙarar da aka shigar bayan zaɓen shugaban ƙasa a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.

Ariwoola ya ce ɓangaren shari’a ba shi da wani shiri na ganin ya yi wa ɗaya daga cikin waɗanda suka shigar da ƙara da kuma waɗanda ake ƙara a ƙararrakin da ke gaban kotu, musamman Tinubu, Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Atiku Abubakar da na Labour Party (LP) Peter Obi.

A wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na Kotun Ƙoli, Festus Akande ya fitar a ranar Laraba, CJN ta ce babu gaskiya a cikin labarin a shafukan sada zumunta.

CJN ya roƙi ‘yan Nijeriya da su bai wa ɓangaren shari’a haɗin kai domin yi wa qasa hidima ga dukkan ƙarfinta.

Ya ce: “’Yan Nijeriya sun bibiyi yadda lamarin ke gudana a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa da farin ciki. Don haka yana da kyau mu ci gaba da riƙe wannan lokaci mu bi shi har zuwa ƙarshe, maimakon mu koma fagen hasashe da jita-jita da ba za ta yi wa kowa komai ba.

“Idan har aka ci gaba da ɗorewar wannan ɗabi’a ta qarya da ƙage, al’ummarmu ba za ta iya samun ci gaban da ake so ba. An kafa kotuna bisa ƙa’ida don biyan buƙatun talakawa; kuma a shirye muke mu yi hakan gwargwadon iyawarmu.

“Doka da ɗaukakar Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya za su kasance a ko da yaushe a kiyaye tare da aiwatar da su a duk wani lamari da ya zo gaban kotu; kamar yadda bayanan da aka gabatar da kuma dokokin da suka ci gaba dole ne a yi amfani da su wajen tantance cancanta ko akasin haka na kowane lamari.

“Ya kamata jama’a su tabbatar da cewa za a yi adalci ga dukkan al’amuran da ke gaban kotuna daban-daban a faɗin ƙasar, ba tare da la’akari da wanda ke da hannu ba.”