’Yan NYSC za su fara karɓar Naira N77,000 daga Maris

Daga MAHDI MUSA MUHANMAD

Darakta-Janar na Hukumar Kula da Masu Yi Wa ƙasa Hidima (NYSC), Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu (mai ritaya), ya bayyana lokacin fara biyan alawus na N77,000.

Shugaban na hukumar NYSC ya bayyana cewa dukkan matasan da ke yi wa ƙasa hidima za su karɓi sabon alawus ɗin su na N77,000 daga watan Maris, 2025.

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da hukumar NYSC ta fitar a ranar Alhamis, 20 ga watan Maris 2025.

Ya ce, hukumar NYSC da Gwamnatin Tarayya suna da alhakin kula da jin daɗin matasan, kuma za su ci gaba da ba da fifiko kan walwalarsu a kowane lokaci.

Darakta-Janar na NYSC ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da yake tattaunawa da matasan da ke yi wa ƙasa hidima a ofisoshin NYSC na yankunan Wuse da Garki a babban birnin tarayya, Abuja.

Birgediya Janar Nafiu, wanda ya yi godiya ga matasan saboda sadaukarwar da suke yi wa ƙasa, ya shawarce su da su kasance masu hankali, jajircewa da ɗa’a yayin da suke hidimta wa ƙasar nan.

Ya yaba wa waɗanda suka kafa shirin NYSC bisa hangen nesa da suka yi wajen ƙirƙiro shi, tare da yin kira ga kowa da kowa da ya marawa shirin baya.

Birgediya Janar Nafiu ya ƙara da cewa, shirin NYSC babbar dama ce da ke samar haɗin kai da sada zumunci, ta yadda matasa masu digiri ke koyon al’adu da darussan rayuwa a wuraren da ba a haife su ba.

Ya kuma jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da koyawa matasa ɗabi’u irin su kishin ƙasa, ɗa’a, biyayya, halayen kirki, basirar jagoranci da aiki tare da juna.

“Daga watan Maris, za ku fara karɓar N77,000 a matsayin alawus na wata-wata. NYSC na da cikakken tsari na adana bayanai, kuma ina tabbatar muku cewa za a biya ku haƙƙokin ku.

“ƙasar nan da hukumar NYSC suna jin daɗin hidimar da kuke yi,” inji Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu.