‘Yan sanda a Kano sun cafke waɗanda ake zargi da ƙona gidan Rarara

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da kama wasu ɓata-gari da ake zargi da cinna wuta a gidan shaharrren mawaƙi, Dauda Kahutu Rarara.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar a Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Kiyawa ya ce sun cafke mutanen ne bisa zargin ƙone wani ɓangare na gidan mawaƙin Jamiyyar APC, biyo bayan samun Nasarar Abba Kabir Yusif na Jamiyyar NNPP a zaɓen Gwamnan Jihar Kano.

Ya ce za su gurfanar da dukkan waɗanda aka samu da hannu cikin lamarin da zarar sun kammala bincike.