‘Yan sanda a Kano sun cafke wani mai damfara da sunan ƙanin Sheikh Abdallah Gadon ƙaya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Kano ta yi nasarar kama wani mutum da ke basaja a matsayin ƙanin shahararren malamin addinin Musulunci a Kano, Sheikh Dr Abdallah Usman Gadon ƙaya, inda yake damfarar mutane masu sai da kayan abinci ta hanyar tura musu alat ɗin banki na bogi.

A ranar 22 ga watan Nuwambar 2024 ne rundunar ‘yan sandan Kano ta samu ƙorafi daga wani mutum mai suna Sunusi Aminu, da ke unguwar Gwale, wanda ya ce a wani mutum da ya kira kansa da Aminu, ya zo shagonsa da misalin ƙarfe 5 na yamma tare da bayyana kansa a matsayin ƙanin Dr. Abdallah Usman Gadon ƙaya.

Mai ƙorafin ya ce, ɗan basajan ya karɓi katan ɗin taliya biyu wanda kuɗinsu ya kai 35,000, inda ya tura masa alat ɗin ƙarya.

Mai shagon ya bar mutumin ya tafi ba tare da tabbatar da sahihancin alat ɗin bogi ba saboda iƙirarin da ya yi cewa ƙanin malam ne.

Daga baya ne kuma ya duba, sai dai bai ga shigowar kuɗin ba wanda hakan ya sa ya shigar da ƙara gaban hukumar ‘yan sanda.

Bayan shigar da ƙarar ne, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya kama runduna a ƙarƙashin jagorancin shugaban rundunar ofishin Dala, SP Abdulrahim Adamu, domin fara bincike.

Nan da nan ne rundunar ta fara aiki tare da cafke wanda ake zargin, Aminu Abdullahi, mai shekaru 50 a duniya da ke zaune a ƙofar Nassarawa a Kano.

Binciken farko, ya nuna wanda ake zargin ya amsa laifinsa cewa shi ba ƙanin Sheikh Dr. Abdallah Gadon ƙaya, kuma yana da ƙwarewa ta tura alat ɗin ƙarya.

Ya ce yana amfani ne da cewa shi ƙanin malam ne wanda hakan ke ba shi damar damfarar mutane ta hanyar karɓar kaya.

Izuwa yanzu akwai ƙorafe-ƙorafe guda 20 da aka shigar a kansa waɗanda suka ce su ma mutumin ya cuce su.

Tuni kuma kwamishinan ‘yan sandan Kano ya ba da umarnin mayar da ƙarar zuwa sashen kula sa manyan laifuka na CID domin cigaba da gudanar da bincike.

Sannan kwamishinan ya gode wa al’ummar Kano kan irin addu’o’in da goyon bayan da suke nuna wa rundunar inda ya yi kira ga al’umma kan su zama masu lura da ‘yan damfara.