Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’in yaɗa labarai na rundunar ƴan sanda DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana wa manema labarai haka kan nasarorin da rundunar ta samu wanjan yaƙi da ɓata gari a jihar.
Haka kuma ya sanar da kama mutane 144 da ake zargi da aikata laifukan da suka haɗa da fashi da makami,satan mutane da waɗanda ake zargin da aikata kisan kai.
DSP Abubakar ya bayyana cewa ƴan sanda sun hallaka yan ta’adda biyar tare da ceto mutane 105 da shanu 16 daga hannun ƴan ta’adda.
Ya danganta nasarar da rundunarsa ke samu na kakkaɓe ɓata gari a jihar da irin goyon bayan da suke samu daga shugaban ƙaramar ƴan sanda na ƙasa da gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa.
Haka kuma DSP Abubakar Sadiq ya yaba da irin gudunmawar da ƴan jaridu ke ba rundunar ƴan sanda a jihar.
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar ƴan sanda a jihar za su cigaba da tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.