Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Yanzu haka mutane bakwai sun shiga hannun ‘yan sanda bisa zargin su da aikata fyaɗe wa yan mata su hudu a garin Kaita, ƙaramar hukumar kaita.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya faɗi haka a yayin da yake gabatar da masu laifin ga manema labarai a ofishin sa.
Ya bayyana cewa dubun ya cika ne bayan da aka kwarmatawa ‘yan sanda a ofishin su da ke garin Kaita inda nan take suka kai sumame a gidan ɗaya da a ke zargi.
ASP Abubakar Sadiq ya ce ‘yan sandan sun sami ‘yan matan da shekarun su na haihuwa bai wuce 14 a gidan da suka tabbatar wa ‘yan sanda da abin da ke afkuwa tsakanin su da mutanan.
“Suma mazan da ake zargi sun amsa laifin su, kuma da zaran mun kammala bincike za a tura su a kotu”Sadiq Aliyu ya ce.
Ya bayyana sunayen waɗanda ake zargi da aikata laifin da suka haɗa da Salisu Ibrahim ɗan shekara 40 da Sabi’u Abdulkarim ɗan shekara 38 da kuma Nuhu Halliru shima ɗan shekara 40.
Akwai kuma Hamza Abdullahi shima mai shekaru 40 da Iliyasu Ibrahim da kuma Idris Abdullahi suma yan shekaru 40 da dukkan su su bakwai yan asalin garin Kaita.