Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wasu matasa da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kashe wani yaro mai suna Salihu Sadi ɗan shekara 12 da haihuwa a garin Dankama dake ƙaramar hukumar Kaita a Jihar Katsina.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar ƴan sanda DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da haka a lokacin da yake gabatar da ƴan ta’addan da sauran wasu masu aikata laifuka daban daban a jihar.
Yace, shi wannan yaro da ya gamu da ajalinsa mahaifiyar sa ta aike shi sayen magani inda matasan da suka haɗa da Muttaƙa Garba da Yusuf Usman suka sace yaron .
A cewar DSP Sadiq,bayan ƴan ta’addan sun kai yaron zuwa wani gida inda suka bugawa iyayen yaron waya cewa yana hannun su sai har iyayen sa sun biya Naira miliyan 25 kafin su sake shi, bayan sun samu bayanin ƙuɗin baza su samu ba,sai dai aka ga gawan yaron da safe a titin.
Matasan a bayanan da suka yiwa manema labarai sun tabbatar da aikata laifin.
Sai kuma Isma’il Isa wani ɗan banga da ƴan sandan suka kama a hanyar Funtua zuwa Zaria ɗauke da bindiga ƙirar AK47 da harsashi guda 12.
DSP Sadiq yace ɗan bangan ya bayyana wa yan sandan da suka kama shi cewa yana kan hanyar na zuwa garin Bakori domin ya iske wani mai suna Mannir da ya sayi bindigan kan kuɗi Naira 900,000.
“Haka kuma ƴan sandan sun kama wasu mutane huɗu a ciki harda ma’aikacin Banki da suka ƙware wajen amfani da tsohon katin waya na MTN suna kwashe kuɗaɗen mutane da suka ajiye a banki” DSP Sadiq yace.
Dubun su ne ya cika a lokacin da ɗaya daga cikin su mai suna Auwal Sani yaje wajen mai sana’ar POS da kuɗin Amurika watau Dala na jabu domin ya canza zuwa Naira.
“Nan ne dubun sa ya cika har ya bada bayanin da yasa jami’an tsaron suka kama abokan huɗɗan shi, su uku”inji DSP Abubakar Sadiq.
Har ilayau, ƴan sanda sun kama wani mutum ɗan shekara 52 mai suna Abdullahi Ali da zargin fasa gilashin motar ɗan majalisa inda ya sace kuɗi Naira 250,000 da wasu huluna na ɗan majalisar.
DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana kama wasu ɓata gari su 15 da zargin sata da sana’ar daba a garuruwan Funtua da Katsina.
A wani sumame da ƴan sandan suka kai a wurare daban daban a garin na Funtua ƴan sandan sun kama wasu cikin waɗannan da ake zargi da sata inji jami’in yaɗa labarai DSP Sadiq.
An kama su ɗauke da buhu 15 na barkono da ake zargi na sata ne da keken hawa guda biyu.