Yan sanda sun ƙaryata rahoton tashin bom a Jos

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Filato ta ƙaryata jita-jitar tashin bom a kusa da tsohuwar babbar kasuwar Jos da aka fi sani da Terminus, a safiyar ranar Talata.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Emmanuel Adesina shi ne ya bayyana hakan bayan ya ziyarci wajen da aka ce an gano wani abu mai kama da bom ɗin gida da ake yaɗawa.

Bayan ƙwararrun jami’an ‘yan sanda masu aikin kwance bom sun binciki wajen da abin ya faru, an gano cewa babu wani abu mai kama da bom da ya fashe a wajen sai tarin ledoji da shara.

Shi ma Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang, cikin wata sanarwa da ta fito daga Kakakin fadar gwamnati, Gyang Bere, ya ƙara musanta jita-jitar da aka riƙa yaɗawa, inda ya buƙaci jama’a su cigaba da gudanar da harkokinsu babu wata fargaba, yayin da gwamnati da jami’an tsaro za su cigaba da aiki, kafaɗa da kafaɗa don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar baƙi ɗaya.

Hukumar kula da harkokin sufuri ta Jihar Filato, ta Plateau Express ita ma ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da jita-jitar da aka riƙa yaɗawa, cewa bom ɗin ya tashi ne a kusa da inda manyan motocinta na safa saga ke tsayawa ɗaukar fasinja a kusa da tsohuwar Babbar Kasuwar Jos ta Terminus.

Ta jaddada cewa motocin hukumar da gwamnati ta tanada domin ɗaukar fasinja a farashi mai rahusa za su cigaba da aikinsu cikin kyakkyawan tsaro da lura.