‘Yan sanda sun ƙaryata shigowar wata baƙuwar halitta cikin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Katsina ta ƙaryata wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo, da ke nuna yadda wata baƙuwar halitta da ba a san ko wacce iri ce ba ta shigo cikin jihar.

A cikin sanarwar da Kakakin rundunar, SP Gambo Isa, ya fitar ya bayyana cewa, an jawo hankalin rundunar ‘yan sanda ta jihar kan wani faifan bidiyo da
ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani da ke nuna yadda wasu baƙin halittu suka mamaye Katsina.

“Hukumar tana so ta bayyana cewa abubuwan da ke cikin bidiyon gaba ɗaya ƙarya ne.

“Wannan wani yunƙuri ne domin a kawo cikas ga zaman lafiya da mutanen jihar ke amfana,” in ji sanarwar.

Don haka Kakakin ya buƙaci jama’a da kada su firgita, su yi watsi da faifan bidiyon na bogi da abubuwan da ke cikinsa.

A wayewar garin Litinin ne aka ga faifan bidiyon na yawo tsakanin al’uma lamarin da ya tada hankalin al’uma. An ji wani mutum a cikin bidiyon yana tarji’i, yana faɗar cewa halittun sun shigo Katsina ne daga wata duniya ta daban, an kuma nuna halittar na tafiya inda ta nufi mutanen dake ɗaukar faifain bidiyon a yayin da suka ranta a na kare.