‘Yan sanda sun bi umarnin kotu kan maido da motocin Matawalle da suka ƙwace

Daga BASHIR ISAH

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta cika umarnin kotun da ya buƙaci ta maido da motocin da ta kwashe a gidajen tsohon Gwamnan Jihar, Bello Matawalle.

A ranar 6 ga watan Yuni jami’an tsaro suka kai samame a gidajen Matawalle da ke Gusau da kuma yankin Ƙaramar Hukumar Maradun inda suka kwahe masa motoci kimanin guda 40 da sauran kadarorinsa.

Jami’an tsaron dai sun ce, sun aikata hakan ne bisa umarnin da kotu ta ba su.

Bayan ‘yan sa’o’i da kwashe motocin ne mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Suleiman Idris, ya fitar da sanarwar cewar jami’an tsaron sun ƙwato motoci 40 a wasu gidaje biyu mallakar Matawalle.

A ranar Alhamis, 15 ga Yuni, 2023, Babbar Kotu mai zamanta a Gusau ta bai wa jami’an tsaron umarnin su maido da motocin da suka kwashe a gidan Matsawalle cikin sa’o’i 48

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar, ya shaida wa majiyarmu cewar, rundunar ta yi wa kotu biyayya inda ta soma mayar da motocin zuwa harabar kotun kamar tadda kotun ta buƙace ta da aikatawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *