Daga BASHIR ISAH
Bayanan ‘yan sandan jihar Kaduna sun nuna ‘yan sandan jihar sun samu nasarar sheƙe gawurtaccen ɗan bindigar nan Yellow Magaji da ya addabi babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya faɗa a ranar Asabar cewa, an kashe Yellow Magaji ne a ranar 24 ga Nuwamban 2021.
A cewarsa, sakamakon bayanan sirri da suka samu ne ya sanya ‘yan sandan Kaduna tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na musamman na tarayya bisa unarnin Kwamishinan ‘Yan sanda CP Mudassiru Abdullahi suka yi dirar mikiya a masaukin baƙi mai suna SIR JOE GUEST INN da ke lamba 8 kan hanyar Sajo da ke Unguwan Maigero, Sabon Tasha a yankin ƙaramar hukumar Chikun, jihar Kaduna, inda aka yi zargin maɓuyan ‘yan fashin daji ne.
Ya ci gaba da cewa, sanin cewa jami’an tsaro sun kewaye su ya sa ‘yan bindigar suka nemi tserewa tare da harba bindiga lamarin da ya sanya su ma jam’ian tsaron suka maida martani.
“Wani gawurtaccen ɗan bindiga da aka fi sani da Yellow Magaji a.k.a Arushe, ya ji rauni sakamakon musayar wutar, haka ma ‘yan’uwansa Yellow Ashana da wasu su ma sun samu rabonsu kafin su tsere.
“Daga bisani an ɗauki wanda ya shiga hannu zuwa Asibitin Koyarwa na Barau Dikko don duba shi kafin a tatsi wasu muhimman bayanai a wajensa amma likita ya tabbatar da ya mutu.”
Jami’in ya ce sakamakon binciken da jami’ansu suka gudanar a maɓuyar ‘yan bindigar sun gano bindiga guda ƙirar AK47 da tarin alburusai da kuma babur ƙirar Boxer ɗaya.
Ya ƙarasa da cewa mutuwar Yellow Magaji babbar nasara ce ga jihar kasancewarsa ɗaya daga cikin gawurtattun ‘yan bindigar da suka addabi babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.