`Yan sanda sun cafke ɓarawon da ke amfanin da katin ATM ɗin jama’a a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta kama wani matashi ɗan damfara wanda ke zuwa banki da nufin taimakon waɗanda ba su iya amfani da na’urar cirar kuɗi ta ATM ba amma daga bisani ya ɓuge da yi masu canjin katin banki ‘ATM Card’ na boge, inda bayan ya yi ma su musayar kati sai ya tafi wajen ma su POS ya yashe masu asusun ajiyarsu na banki.

Aminu Rabiu dake zaune a Ɗanɗagoro ya shigar da ƙorafi a babban ofishin ‘yan sanda dake birnin Katsina, inda Aminu ya bayyana wa ‘yan sanda cewar ya je bankin First Bank don cirar kuɗi amma sai ya roƙi wani mutum da ya taimaka masa bayan ya bar bankin sai ya lura cewar mutumin ya yi masa musayar kati inda ya kwashe masa asusun ajiyarsa da ke ɗauke da kuɗi Naira 153,000.

SP Isa ya bayyana cewar bisa bayanan sirri da rundunar ta samu sun samu nasarar cafke wani Aliyu Abdullahi da ke zaune a kasuwar Mata dake ƙaramar hukumar Funtua wanda ya shahara wajen kwashe wa al’umma kuɗaɗen su da su ka ajiye a banki da sunan zai taimake su wajen cire kuɗi ta hanyar yi ma su musayar katin banki.

SP Isa ya bayyana cewar dabarar da Aliyu ke yi don cire wa al’umma kuɗi daga banki shi ne ya kan je banki wajen na’urar cirar kuɗi wato ATM sai ya tsaya da nufin idan wanda bai iya amfani da na’urar ba ya zo sai ya karɓi katinsa da lambar sirrinsa da nufin zai taimaka masa amma sai ya yaudari mutum ya yi masa musayar kati, inda ya ke karɓe katin mai neman taimaka ya musanya masa da wani katin na daban daga baya sai ya je wani bankin ko wajen masu sana’ar POS ya kwashe wa al’ummar da ba su ji ba su gani ba kuɗi

Asirin sa ya tonu ne bayan da ya damfari wata tsohuwar ma’aikaciyar gwamnati a Katsina mai suna Maryam Sale bayan da ta je banki don cire kuɗin sallamar aikinta da gwamnati ta turo mata.

Maryam ta nemi ɗan damfarar akan ya taimaka mata ta cire kuɗi amma ko da ya lura akwai kuɗi sama da Naira miliyan ɗaya a asusunta sai ya yi mata musayar kati, inda ya tafi wajen ma su POS ya kwashe mata zunzurutun kuɗi har Naira 1,846,000.

Da aka tambayi Aliyu me ya yi da kuɗin sai ya ce ya sayi mota ƙirar Honda Henesy akan kuɗi Naira 500,000 ya kuma sayi sabon babur ƙirar TVZ a kan kuɗi Naira 323,000 a yayin da ya kashe sauran ragowar kuɗin.

Daga ƙarshe rundunar ta ce tana ci gaba da bincike kafin miƙa mai laifin gaban kuliya.