‘Yan sanda sun cika hannu da waɗanda suka ɓarnata gidan Rara a Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Usaini Mohammed Gumel, ta yi nasarar cafke wasu mutane kimanin su 21 da ake zargi da hannu wajen ɓarnatawa da sace kayan shahararren mawaƙin nan, Dauda Adamu Kahutu da akafi sa ni da Rarara da ɓata wani ɓangare na sakatariyar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC da ke hotoro cikin birnin Kano.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Kakakin rundunar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya fitar ga manema labarai.

Sanarwar ta ce, a ranar 20-03-2023 da misalin ƙarfe 2 na rana rundunar ta samu sanarwar cewa wasu gungun ‘yan dabar siyasa da ke murnar lashe zaɓen a Kano sun sauya akala tare da zuwa gidan Rarara da ke Unguwar Hausawa kan titin gidan ajiyar namun daji a Kano tare da wajen shirya waƙoƙinsa da yake a ofishin sa da ke gidan Dan Asabe shi ma a kan titin na gidan zoo.

Sannan kuma matasan ba su tsaya nan ba inda suka ƙarasa ofishin mawaƙin da ake ma laƙabi da 13×13 dake kallon ƙofar shiga gidan ajiyar namun dajin na Kano nan take suka cinna ma wani bangaren na gidansa wuta tare da ɓata ofishin 13×13 da sutudiyon na sa wanda ya yi sanadiyyar salwantar da kayan milyoyin naira.

Sanarwar ta ƙara da cewa bayan ɓarnar da suka yi ma mawaƙin, sun kuma yi awan gaba da motoci guda biyu da lakata kayan gurin, kana suka farmaki wasu shaguna huɗu a yankin.

Kiyawa ya kuma tabbatar da cewa wasu gungun sun Kuma kai hari a sakatariyar jam’iyyar APC da ke a Hotoro inda suka lakata ɓangaren ofishin tare da sace wasu kayayyaki.

Kakakin ya bayyana cewa lokacin da hukumar ta samu sanarwar abin da ya faru sun hada jami’an tsaro tare da masu kashe gobara wanda nan take suka garzaya guraren suka kuma kashe wuta cikin nasara.

Ya ce a wannan lokaci an wawu mutum 21 da ake zargi da hannu a harin da aka kai gidan mawaƙin da kuma wasu mutum takwas da ake zarfi da hannu a harin da aka kai ofishin jam’iyyar APC da ke Hotoro.