‘Yan sanda sun daƙile harin ‘yan bindiga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar daƙile wani harin ‘yan bindiga da yammacin ranar Juma’a tare da ƙwato dabbobi kimanin 350 daga hannun ‘yan ta’adda.

Kakakin rundunar SP Gambo Isa ne ya sanar da hakan a yau Asabar cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a birnin Katsina.

SP Isa ya bayyana cewar sun samu nasarar fatattakar ‘yan bindigar ne sakamakon kiran gaggawa da rundunar ta samu da yammacin ranar Juma’a, inda mazauna ƙauyen Nassarawar Bugaje da ke a ƙaramar hukumar Jibiya ta jihar Katsina suka sanar da rundunar cewar gungun ‘yan ta’adda ɗauke da muggan makamai a kan babura sun mamaye garin tare da yin harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa.

Rundunar ba ta yi wata-wata ba, inda ‘yan sandan dake yaƙi da masu garkuwa da mutane ta tunkari ‘yan bindigar.

“An tura da ‘yan sanda masu yaƙi da garkuwa da mutane a ƙauyen inda aka yi musayar wuta da ‘yan ta’addar.

“Salo da ƙwarewa da jami’an ‘yan sanda suka nuna a yayin gumurzun ya sa ‘yan bindigar guduwa tare da barin baburan su da kuma shanun da suka sato,” inji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa ‘yan sandan sun samu nasarar ƙwato dukkan dabbobin da ‘yan bindigar suka yi ƙoƙarin arcewa da su wanda suka haɗa da shanu ɗari 200 sai tumaki kimanin ɗari 150.

“A yayin arangamar ‘yan sanda dake yaƙi da masu garkuwa da mutane sun samu nasarar ƙwato dabbobin da ɓarayin su ka sace wanda su ka ƙunshi shanu 200 gami da tumaki 150.”

SP Isa ya ƙara da cewa an samu sababbin babura guda 2 da ‘yan ta’addar suka gudu su ka bari da sauran kayan amfanin da yau da kullum.

A ƙarshe, kakakin rundunar ya bayyana cewar ana ci gaba da bincike a kan lamarin.