‘Yan sanda sun damƙe ɗan shekara 25 bisa zargin yin lalata da akuya a Jigawa

‘Yan sanda a Jihar Jigawa sun damƙe wani ɗan shekara 25 kan zargin yin lalata da akuya a yankin Ƙaramar Hukumar Gwaram da ke jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu, shi ne ya bayyana aukuwar hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Dutse a ranar Juma’a.

A cewar jami’in ‘yan sandan, sun cafke wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 1 na dare sa’ilin da suke sintiri a bakin aiki a cikin garin Gwaram.

Ya ce, wanda ake zargin mazaunin Kunnadi kwatas ne, kuma an kama shi ne a daidai lokacin da yake tsaka da yin lalata da wata akuya.

Ya ƙara da cewa, yanzu haka sun soma bincike kan lamarin, sannan bayan kammalawa za su maka wanda ake zargin a kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *