‘Yan sanda sun damƙe masu safarar sassan jikin mutum a Kwara

Daga BASHIR ISAH

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kwara ta ce, ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da safarar sassan jikin mutum a jihar.

Rundunar ta ce, sakamakon matsawa da ta yi da bincike kan ɓacewar wasu ‘yan mata, a nan ta gano Femi Adeniji da Shittu Abdulmalik a matsayin masu safarar sassan jikin mutum ta kuma kama su.

Cikin sanarwar da ta fitar ta hannun jami’inta na hulɗa da jama’a, SP Okasanmi Ajayi (anipr), runduna ta ce ba za ta lamunci ci gaba da aukuwar miyagun ayyuka ba a jihar Kwara, don haka ta shawarci maɓarnata a ko’ina suka a faɗin jihar da su gaggauta ficewa daga jihar tun kafin ta gamu da su.

Kazalika, ganin yadda harkokin matsafa ke ƙamari a jihar, musamman a tsakanin matasa masu burin yin arziki ko ta halin ƙaƙa, ya sanya rundunar ta yi kira ga iyayen yara da su sanya ido sosai a kan ‘ya’yansu.

Rundunar ta ce an samu aukuwar kisa a jihar a ranar 14 ga Satumban 2021, yayin da wata mai suna Rianat Yusuf daga yankin Amuyo a Offa ta bar gida da nufin zuwa sayen ƙuluƙuli, amma tun wancan lokaci ba a ga dawowanta ba.

Haka ma rundunar ta samu rahoton ɓacewar wani yaro mai suna Yusuf Taofeek a yankin Amuyo na  Offa wanda mahaifinsa ya kai rahoton ɓacewarsa ga babban ofishin ‘yan sandan jihar.

Sanarwar rundunar ta ce, ko da rundunar ta matsa bincike kan waɗannan batutuwa, daga bisani ta gano wata gawar mace, babu kai da hannuwa a cikin wani kangon gini a yankin Amuyo wanda a ƙarshe mahafin yarinyar nan da aka ce ta ɓace, ya iya tantance gawar kan cewa ‘yarsa ce.

Rundunar ta ce, a halin bincikenta ne ta damƙe wani mai suna Femi Adeniji a nan yankin da lamarin ya auku wanda ya amsa cewa lallai kai da kuma hannuwan gawar Rianat Yusuf da aka gano suna wurinsa.

Haka nan, ya sake shaida wa ‘yan sanda cewa, ya sayar da hannu guda ga wani wanda a halin yanzu ake nemansa ruwa a jallo kan N20,000.

A cewar rundunar, wani mai suna Shittu Abdulmalik Wale da ta kama a yankin, shi ma ya amsa cewa ya yi amfani da ɗaya hannun marigayiyar wajen sarrafa sabulun tsafin neman kuɗi.

Yayin da ta ba da tabaccin cewa tana nan tana ci gaba da gudanar da bincike kan wannan badaƙalar, rundunar ta ce za ta maka waɗanda take zargin a kotu bayan kammala binciken nata.

Da wannan ne Kwamishinan ‘Yan  Sanda Jihar Kwara,  CP Tuesday Assayomo, ya shawarci matasa da su guji neman kuɗi ta kowace irin mummunar hanya, yana mai cewar ita rayuwa sai an wahala kafin a ji daɗi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *