’Yan sanda sun damƙe soja yana fashi da makami a Yobe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Dubun wani soja ta cika inda aka kama shi tare wa wasu mutum biyu bayan sun aikata fashi da makami a garin Damaturu, Jihar Yobe.

’Yan Sanda sun cafke sojan da abokan fashin nasa ne bayan sun kutsa gida wata mata a unguwar Sabon Pegi da tsakar dare ɗauke da bindiga ƙirar AK 47 da sauran muggan makamai suka yi mata fashi.

An kama sojan da abokan fashinsa ne bayan sun yi wa matar awon gaba da mota ƙirar Peugeot 307 da tsabar kuɗi N250,000 da kuma wayar hannu ƙirar Nokia.

“Bayan an kama su, sun shaida wa ’yan masu bincike cewa suna so ne su sayar da motar su raban kuɗin. Za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike,” inji Kakakin ’yan sandan Jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim.

Ya ƙara da cewa, ’yan fashin sun yi wa matar da ɗanta mai shekara 17 rauni bayan sun ɗaure su da wata waya.

ASP Dungus ya bayyana cewa, an kama biyu daga cikin ’yan fashin ne a garin Damaturu, na ukunsu kuma wanda motar ta ke hannunsa an kama shi ne a garin Darazo na Jihar Bauchi.

Ya ce, ’yan sanda sun yi nasarar kwace makaman ’yan fashin da kuma duk kayan da suka yi fashi a gidan da suka shiga.

Ya bayyana cewa, sojan da aka maka yana aiki ne da Runduna ta 2 ƙarƙashin Rundunar Operation Haɗin Kai da ke aiki a Damaturu, sauran kuma matasa ne da ke zaune a garin.

Yanzu haka sojan da abokan fashin nasa suna fuskantar zargin shiga gida ba da izini ba, aikata fashi da makami da sauran laifuka.

A cewarsa, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Yobe, Haruna Garba, ya shawarci mazauna jihar da su kasance masu lura a abin da faruwa a zagaye da su, tare da taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai domin magance miyagun laifuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *