‘Yan sanda sun damƙe mutumin da ya halaka matarsa a Sule Tankarkar

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

‘Yan sanda a yankin ƙaramar Hukumar Sule Tankarkar da ke yankin Masarautar Gumel a Jihar Jigawa sun damƙe wani mutun mai suna  Bulama Muntari Ubale ɗan shekara 65 a duniya bisa zarginsa da yi wa matarsa duka da sanda har ta ka ga ya halakata. 

Asirin Bulama ya tonu ne bayan da wani maƙocinsu ya ji ihun matar tasa, inda maƙocin mai suna Yusuf Zubairu mai kimanin shekaru 26 ya kai agaji a Rugar Fulanin Mailefe da ke cikin ƙauyen Baldi, inda ya taras ya yinwa matar tasa mai suna Fatima Harɗo Dare ‘yar shekara 23 mummunan rauni a kanta. A ƙoƙarin raba su ne shi ma aka ji masa mummunan rauni akan sa.

Yusuf Zubairu ya ce a lokacin da ya isa wurin Fatima Harɗo ko numfashi ba ta yu, domin ya yi mata mummunan rauni.

Ya ƙara da cewar kafin zuwansa wurin ma akwai wata mata mai suna Rabi Lawan da suke maqotan juna da ta je domin rabasu ita ma Bulama bai barta haka ba sai da ya yi mata shaida a kanta. 

Yayin da ‘yan sanda suka sami labarin faruwar labarin sai suka yi wa wajen tsinke da nufin kama wanda ake zargin. Kuma suka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Gumel.

 Zuwansu asibiti ke da wuya likita ya tabbatar da mutuwar Fatima, amma ita Rabi tana kwance a asibiti likitoci na ƙoƙarin ceto rayuwarta.

Tuni dai ‘yan sanda suka kame Bulama domin gudanar da binciken lamarin.