
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Kaduna, ta kama mutum 580 bisa manyan laifuka da suka haɗa da garkuwa da mutane, fashi, ƙwacen waya da kuma sata.
Kwamishinan ƴan sandan, Muhammad Rabi’u ya bayyana hakan a ranar Talata a yayin ganawa da manema labarai akan nasarorin da suka samu.
Ya ce an yi kamen ne daga ranar 31 ga watan Disambar 2024 zuwa 10 ga Fabrairun 2025 ta wasu atisayen sirri da kuma haɗin-gwiwar wasu hukumomin tsaro.
Cikin waɗanda aka kama akwai masu garkuwa da mutane guda 20, ƴan fashi 32, masu ƙwacen waya 320 da kuma masu satar mota guda biyar.
Haka kuma jami’ansu sun ceto mutane 30 da aka yi garkuwa da su tare da haɗa su da iyalansu.
Kwamishinan ya kuma ce sun ƙwato babura guda 34, motoci 10 da kuma bindigu ƙirar AK47 guda huɗu.
Sauran abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da ƙananun bindigogin ‘submachine gun’ da ‘pistol’ da alburusai 28 da buhunan wani sinadari da ake zargin tabar wiwi ce aciki.
Kwamishinan ya jaddada aniyar rundunar ta cigaba da tabbatar da zaman lafiya a jihar, ya na mai kira ga al’umma da su cigaba da bai wa jami’an haɗin-kai waje ba su bayanan da za su taimaka masu wajen daƙile ayyukan ta’addanci.