‘Yan sanda sun kama ɗaliba ƴar shekara 17 da ta yi ƙaryar an sace ta an kashe

Daga BELLO A. BABAJI

Jami’an ƴan sandan Jihar Imo sun yi nasarar kama wata ƴar shekara 17 mai suna Jesse Chidiebere wadda ɗaliba ce a Jami’ar jihar, IMSU wacce ta yi ƙaryar garkuwa da kuma mutuwa.

Henry Okoye, wanda shi ne Kakakin rundunar ƴan sandan, ya faɗa a cikin wata sanarwa cewa sun samu rahoton zargin ɓacewar yarinyar a ranar Asabar da ta gabata.

Chidiebere ta bayyana wani saƙo ta wattsapp da ke nuna cewa an yi garkuwa da ita kuma an kashe ta wanda hakan ya sa iyalanta suka garzaya ofishin ƴan sandan don isar da rahoto.

Daga nan ƴan sandan suka fara gudanar da bincike a ranar Lahadi inda suka gano cewa bidiyon wasa ne ta shirya da ake kira da ‘prank’ don sanya shi a kafafen sada zumunta.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Aboki Ɗanjuma ya bayyana damuwarsa kan yadda yarinyar ta yi wasa da hankalin mutane da ya haifar tsoro da fargaba acikin al’umma.

Ya gargaɗi iyaye da su ke kwaɓar ƴaƴansu kan yin ire-iren wasannin da suka ƙunshi haɗari da ka iya haifar da ruɗani acikin al’umma.

Ya kuma ce zasu cigaba da yaƙar ire-iren ayyukan don tabbatar da tsaro ga al’umma a jihar.