’Yan sanda sun kama ɓarayi 50 a gobarar kasuwar Maiduguri 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Jihar Borno ta kama wasu mutane 50 da ake zargi da yin sace-sace a kasuwar Monday Market ta Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), Kamilu Shatambaya ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a ranar Laraba a Maiduguri.

Ya ce jami’an rundunar da aka tura domin kare rayuka da dukiyoyin da gobarar ta afku a kasuwar, sun kama waɗanda ake zargin ne a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Ya ce waɗanda ake zargin sun yi awon gaba da kadarorin waɗanda abin ya shafa a lokacin da ‘yan kwana-kwana da jami’an tsaro ke fafutukar kashe gobarar.

Kakakin ya ce rundunar ta kuma kama wani mutum mai suna Sadiq Ibrahim mai shekaru 20 da laifin ƙona wata motar rundunar haɗin gwiwa ta CJTF.

Ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.

A cewarsa, kwamishinan ‘yan sanda, Mista Abdu Umar ya jajantawa gwamnatin jihar tare da yin kira ga waɗanda abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu domin gwamnati na yin duk mai yiwuwa don rage raɗaɗin da suke ciki.