Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ƴan ta kama wasu manyan ƴan ta’adda uku da wasu masu aikata mayan laifuka a Jihar Katsina.
Haka kuma, sun samu nasarar kama wani ƙasurgumin ɗan fashi da makami da masu sace wayoyin wutar lantarki masu amfani da hasken rana.
Wata takarda ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce ƴan ta’addar da suka zo hannun hukumar an kama su ne a lokuta mabanbanta.
Abubakar Nasiru ɗan asalin ƙaramar hukumar Daura, an kama shi ne bayan haɗa kai da yayi da wasu ƴan ta’adda inda suka kai hari a ƙauyen Maza na ƙaramar hukumar Ƙafur.
Bayan hare-haren da suka yi, sun samu nasarar sace mutane uku inda suka karɓi Naira miliyan 13.
Abubakar Nasiru dai ya amsa laifinsa, ya kuma ce, ce ya karɓi Naira miliyan biyu a matsayin nashi kason.
Sai Ibrahim Isah na ƙauyen na ƙaramar hukumar Charanchi da wasu ƴan ta’adda da suka yi garkuwa da wani yaro inda suka tuntuɓi mahaifin yaron, Malam Bello Sani da ya biya miliyan ɗaya kafin su saki yaron wanda bayan ya biyan kuɗin fansar ne sai suka kashe yaron.
Haka kuma, rundunar da haɗin-gwiwar takwararta ta Jihar Gombe sun yi nasarar kama wani babban ɗan ta’adda mai suna Nasiru sunusi na ƙauyen Gidan Dauda a karamar hukumar Ƙanƙara.
Ya haɗa kai ne da wasu ƴan ta’adda uku da ake neman su ruwa a jallo wanɗanda suka yi garkuwa da wani mutum inda suka amshi Naira miliyan 8 amma kuma suka kashe shi .
Nasiru sunusi ya tabbatar wa ƴan sanda da aikata laifin, ya na mai cewa ya fi aikata ta’addanci a Jihohin Gombe, Taraba da Lagos.
Shi kuwa Nuhu Haruna ɗan shekara 16 daga ƙauyen Fenza a ƙaramar hukumar Dutsinma an same sa da laifin kisan kai.
Wani saɓani ya haɗa shi da kishiyar mahaifiyarsa Rabi Haruna yar shekara 40 da haihuwa inda nan take ya yi sanadiyar ajalinta.
ASP Sadiq Aliyu ya ce, da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban ƙuliya.