‘
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Jihar Kaduna ta ce ta kama masu garkuwa da mutane guda uku da suka fito daga wata sananniyar daba da ke ayyukanta a babbar hanyar Abuja-Kaduna da wasu maƙotan jihohi.
Cikin wata sanarwar da Kakakin rundunar, ASP Mansir Hassan ya fitar, ya ce tawagar Fushin Kada ne ta gudanar da atisayen a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2024 bayan samun wani bayani na sirri.
Waɗanda aka kama sune; Muhammad Lawal Abubakar da Abubakar Isa masu shekaru arba’in-arba’in da kuma Sama’ila Sa’idu mai shekaru 65.
Ya ce, an kuma ƙwato bindiga mai ƙirar AK-47 da wata fankon mujalla daga ƴan bindigar.
Ƴan ta’addar sun kuma amsa laifukansu inda suka ce suna da hannu acikin ayyukan garkuwa da mutane da waɗansu hare-hare da aka kai a hanyar Abuja-Kaduna akan matafiya da mazauna yankunan.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ibrahim Abdullahi ya yaba da ƙoƙarin jami’an tare da kira ga al’umma da su ruwaito duk wani abin zargi da suka gani ga rundunar don tabbatar da tsaro ga rayuka da dukiyoyinsu.