Daga UMAR GARBA a Katsina
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Katsina, ta bayyana cewa ta kama mutane takwas da take zargi bisa ƙona motar jami’anta masu kula da zirga-zirgar ababen hawa a titunan jihar.
Lamarin dai ya faru ne a titin Ƙofar Guga ɗaya daga cikin manyan hanyoyi a babban birnin jihar da aka fi samun cinkoson ababen hawa.
Rahotanni sun bayyana cewa rikici ya ɓarke tsakanin jami’an rundunar (MTD) da kuma masu ababen hawa dake amfani da hanyar.
‘Yan sandan sun yi ƙoƙarin kama wani mai babur da ya karya dokar tuƙi, sai dai wasu mutane dake kan titin sun hana a kama mai laifin.
Masu amfani da hanyar sun zargi jami’an ‘yan sandan dake kula da zirga zirgar ababen hawa da karvar na goro, gami da cin zarafin masu babura a duk lokacin da suke aiki kan titunan birnin lamarin da ya kai ga ƙone masu motar aiki ƙurmus.
Sai dai a samamen da rundunar ta kai jiya Laraba ta bayyana cewa ta kama mutane takwas da ake zargi da wannan aika aika.
Kakakin rundunar Abubakar Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Alhamis, inda ya ce, “Gaskiyar abunda ya faru shine wani mai babur dake ƙoƙarin kauce wa jami’an dake kula da zirga zirgar ababen hawa don kada su kama shi lokacin da suke gudanar da aikinsu ya faɗi a kan titi.
“Sai dai bayan da ya gudu ya bar babur ɗinsa wata babbar mota dake wuce wa kan hanyar ta bi ta kan babur ɗin, daga nan sai wasu ɓata gari suka yi amfani da yanayin da ake ciki inda suka taimaka masa ya gudu su ka kuma bankawa motar sintirin jami’an wuta.” Inji shi
Ya ci gaba da cewa samun rahoton halin da ake ciki keda wuya sai babban jami’an dake kula da ƙwaryar birnin ya jagoranci wata tawagar ‘yan sanda zuwa wajen da lamarin ya faru, inda bayan shawo kan lamarin aka damƙe mutane takwas da ake zargi da tada hatsaniyar.