‘Yan sanda sun kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a kisan wani babban soja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Rundunar Ƴan sanda ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi kan kisan tsohon shugaban rundunar soji na ƙasa kuma jami’i Mai ritaya, Burgediya Janar, Harold Udokwere.

Jaridar ‘Blueprint’ ta ruwaito cewa an kashe babban sojan ne a gidansa dake layin Sanga, a rukunin gidajen Sunshine, a unguwar Lokogoma dake Abuja a yayin wani fashi da wasu ƴan bindiga suka kai yankin.

An samu bayanin ne a wani faifan bidiyo da ke ɗauke da rubutu inda waɗanda aka kama sun haɗa da; Ibrahim Rabi’u, mai shekaru 33 daga Ƙaramar Hukumar Dala, Jihar Kano mazaunin Rasha Apo Roundabout, sai Nafi’u Jamil mai shekaru 33 daga Ƙaramar Hukumar Tofa, Jihar Kano, sai Aliyu Abdullahi mai shekaru 47 ɗan Ƙaramar Hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara sannan sai Muhammed Nuhu mai shekaru 28 ɗan Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano mazaunin Apo primary school.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, waɗanda a ke zargin, sun amsa laifukan da aka tuhume su a kai na fashi da kuma kisan mamacin.

Ɓarayin sun ce sun kashe mamacin a yayin da ya ɗakko ƙaramar bindigarsa ta fistol ya yi nufin harbin su, a inda suka yi nasarar kashe shi wajen kare kansu.

Sun ƙara da cewa, sun sace na’urorin ‘Laptops’ da wayoyi da wasu abubuwa masu tsada.

Leave a Reply