‘Yan sanda sun kama tirela maƙare da matasa ɗauke da muggan makamai a Ogun

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sanda a Jihar Ogun, ta yi nasarar kama wasu gungun matasa a tirela ɗauke da wasu muggan makamai a jihar.

Kakakin rundunar, Omolola Odutola ya bayyana hakan, inda ya ce an kama su ne a ranar Asabar ƙarƙashinsa jagorancin Kwamishina Lanre Ogunlowo, a yankin iyakan Alapako da Onigari dake iyaka da Jihar Oyo.

A sanarwar da Odutola ya fitar, Kwamishinan ya ce sun gano cewa tawagar matasan ba ta da takamaiman wajen zuwa ko kuma bada gamsashshen bayani akan zirga-zirgarta.

Daga nan ne sai ya umurci a yi bincike akansu, wanda hakan ya kai ga ƙwato makamai a hannunsu da suka haɗa da barandami da adduna da wuƙaƙe da wasu kayayyakin tsafi.

Tuni dai Kwamishinan ya bada umarnin a tsare matasan tare cigaba da gudanar da bincike akan su.

Ya kuma ce, duk wanda aka samu da laifi a cikin mummunan aikin, za a maka shi a kotu don ya fuskanci hukuncin doka.

Kazalika, rundunar ta sha alwashin cigaba da aiki tuƙuru wajen bai wa rayuka da dukiyoyin al’umma kariya a jihar.