‘Yan sanda sun kuɓutar da ɗalibai 2 daga ɗaliban da aka sace a Yauri

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce, ta yi nasarar kuɓutar da wasu ɗalibai biyu da aka sace na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Yaurin Jihar Kebbi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Hussaini Rabiu ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudana ranar Lahadi.

Rabiu ya ce, “A ranar 31 ga Yuli 2021, Jami’an‘ Yan Sanda na rundunar Operation Restore Peace da aka tura yankin Ɗansadau na Ƙaramar Hukumar Maru don yaƙi da ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane, sun ceto Maryam Abdulkarim ‘yar shekara 15 daga ƙaramar hukumar wushishi ta Jihar Neja da Faruk Buhari ɗan shekara 17 daga garin Wara a jihar Kebbi a wani daji da ke kusa da ƙauyen Babbar Doka na Masarautar Ɗansadau.”

A cewarsa, bincike ya nuna ɗaliban da aka kuɓutar din na daga cikin ɗaliban da aka sace na Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Yauri, jihar Kebbi.

Ya bayyana cewa an kai waɗanda abin ya shafa asibiti domin duba lafiyarsu, kuma bayani ya isa babban ofishin ‘yan sanda da ke Gusau.

Kazalika, ya bayyana cewar za a miƙa ɗaliban ga gwamnatin jihar Kebbi ta hannun rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *