Daga UMAR GARBA a Katsina
Rundanar ƴan sandan Jihar Katsina ta musanta wasu rahotanni dake cewa ƴan bindinga sun tarwatsa mutane a garin Ɗan Ali dake ƙaramar hukumar Ɗan Musa a jihar, a lokacin da suke sallar juma’a.
Rundanar ta ce an ƙirƙiri labarin ne don a jefa al’ummar yankin cikin firgici da razani, don haka rundunar ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da labarin.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa, ƴan bindinga ɗauke da muggan makamai sun yi dirar mikiya a garin Ɗan Ali a ranar Juma’a, 4 ga watan Oktoba, inda suka riƙa bi masallatai suna tarwatsa jama’a don hana su gudanar da sallar juma’a.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta raba wa manema labarai, ta ce ƴan bindigar sun yi yunƙurin shiga garin ne don yin garkuwa da wasu manoma wanda ba su yi nasara ba.
“Ɗaukin gaggawa da jami’an ƴan sanda da sojoji da jami’an tsaron KSCWC suka kai wa garin ya daƙile mummunar aniyar maharan tare da bai wa manoman kariya”, inji sanarwar.
Saboda haka ne kakakin rundunar, CP Aliyu Abubakar, ya yi kira ga al’umma da su yi watsi da ƙirƙirarren labarin da kuma riƙa tantance labari kafin yaɗa shi.
CP Abubakar ya ce, rundunar ƴan sandan ta duƙufa wajen kare lafiya da dukiyoyin al’ummar jihar.