
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Laraba ne rundunar ƴan sandan Legas ta ce ta tono gawar wani ɗalibi da ya kammala karatu a Jami’ar jihar (LASU), mai suna Ademola Ogunbode.
An binne gawar ɗalibin ne mai shekaru 28 a wani ƙaramin kabari a bayan katangar jami’ar dake Ojo.
Tun a ranar 16 ga watan Junairu ne mamacin, wanda ya yi karatu a tsangayar Nazarin Siyasa, ya ɓata, wanda hakan ya sanya jami’an ƴan sanda kama wasu mutane huɗu da ake zargin su da hannu a kisan ɗalibin na ajin 2024.
Ana zargin su da cire baki ɗaya kuɗaɗen da ke asusun mamacin tare da raba su a tsakanin su.
Jami’in yaɗa labaran rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, wanda ya na ɗaya daga cikin ƴan sandan da suka je wajen da aka binne gawar, ya ce ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ne ya nuna wa jami’an kabarin.
Bayan samun rahoton ɓatan mamacin ne a ranar 16 ga watan Junairu, sai Kwamishinan ƴan sandan jihar, Mista Oluhundare Jimoh, wanda ya koma aiki a ranar 18 ga Fabrairu, ya umarci ofishin bincike na jihar da ya yi bincike akan lamarin.
Jami’in labaran ya kuma ce za su kamo sauran waɗanda ke da hannu acikin kisan a yayin da suke ƙoƙarin kammala binciken.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa, za a yi adalci akan waɗanda ake tuhuma da aikata laifin.
Haka kuma rundunar ta jajenta wa iyalan mamacin bisa rashin da aka yi masu, da kuma miƙa godiyarsu ga gwamnatin jihar wajen daƙile ayyukan ta’addanci.