‘Yan sanda za su binciki yadda aka tsare yaran zanga-zanga cikin ƙasƙanci

Daga BELLO A BABAJI

Sufeton ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya gayyaci manyan jami’ai da suka haɗa da DCs da CID da jagororin cibiyoyin bincike kan irin kulawar da aka bai wa yara marasa galihu da aka tsare su a hannun ƴan sanda.

Hakan zuwa ne bayan gabatar da yaran da aka yi cikin mawuyacin hali a ranar Juma’a, a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja.

Masu zanga-zangar sun kasance cikin halin rashin samun isasshen abinci bayan watanni uku da aka tsare su wanda hakan ya haifar da cecekuce acikin al’ummar Nijeriya.

Wata sanarwa da Kakakin ƴan sandan, Muyiwa Adejobi ya fitar, ta ce Sufeton ya bada umarnin a gudanar da bincike mai zurfi game da irin kular da aka bai wa yaran a lokacin da suke hannunsu.

Adejobi ya ce tuni aka aika da rahoton binciken ga Sufeton wanda a yanzu ya na ƙasar Glasgow don halartar wani babban taro.

Rundunar ƴan sandan ta jaddada aniyarta na cigaba da kiyaye ƙa’idojin doka da oda tare da tabbatar da gaskiya da adalci musamman ga marasa ƙarfi acikin al’umma.

A ranar Litinin ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin a gaggauta sakin yaran da aka tsare ta bakin Ministan Labarai, Mohammed Idris.

Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya bada umarnin ne ba tare da la’akari da hukuncin doka dake kan yaran ba.

Shugaban Tinubu ya kuma bai wa Ma’aikatar Jin-ƙai ta bai wa yaran kulawar da ta dace tare da damƙa su wa iyalansu cikin aminci, sannan ya bada umarnin samar da kwamiti a ƙarƙashin Ma’aikatar da zai yi bincike game da lamarin yaran.