’Yan sandan Bauchi sun cafke soja da tabar wiwi

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Wani da aka ayyana a matsayin jami’in soja mai suna Yusuf Gongpolai Adams, da aka cafke da pasul-pasul guda 81 na tabar wiwi yanzu haka yana tsare a kurkukun ‘yan sanda na jihar Bauchi.

Gongpolai, wanda yake jami’in soja ne na rundunar soji dake bataliya ta 145 a jihar Abiya, an damƙe shi ne a ranar 6 ga wannan wata na Fabrairu, 2022 akan hanyar Bauchi zuwa Darazo cikin wata mota ‘Toyota Highlander’.

Da yake nuna shi wa manema labarai a garin Bauchi a ranar Talata da ta gabata, kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Umar Mamman Sanda ya bayyana cewar, Yusuf Adams a yanzu yana karatu ne a makarantar Nazarin Muhalli Da Fasahar Kimiyya ta Soji dake jihar Binuwai.

CP Umar Sanda ya kuma bayyana cewar, magwadai da aka samu tattare da jami’in sojan, sun haɗa da tabar wiwi pasul guda 81, da rigar soji saiti guda.

Sauran kayayyaki da aka samu a tattare da shi, akwai hular soji, wani ƙaton akwati mai ɗauke da tufafi, har ma da kayayyakin suddabaru na kariya da ƙifaɗi (charms), kuma da zarar an gama bincike, za a gurfanar da shi a gaban kuliya.