‘Yan sandan Kano sun kama jabun kuɗi na Naira 129bn

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano, ta kama wasu mutane uku da aka samu jabun kuɗaɗe a wajensu da adadinsu ya kai Naira biliyan 129 da miliyan 542 da kuma naira 824 (N129,542,824,000).

Kuɗaɗen sun haɗa da jabun Dalar Amurka, CFA da kuma Naira.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke holen waɗanda ake zargin a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai.

SP Kiyawa ya ce sun samu nasarar kama mutum na farko mai suna Ahmad Abdullahi, ɗan shekaru 30 mazaunin ƙaramar hukumar Kaga ta jihar Borno, bayan samun sahihan bayanan sirri, inda kwamishinan yan sanda jihar, CP Salman Dogo Garba ya tura dakarun ƴan sanda ƙarƙashin jagorancin SP Abdurrahim Adamu, wanda shi ne baturen ƴan sandan Gwale don faɗaɗa bincike kan lamarin.

A ranar 1 ga watan Disamban 2024 ne rundunar ta fara kama wani mai suna Nura Ibrahim Sharaɗa da kuma Muhammad Mukhtar Hotoro, inda bincike ya kai ga kamo wanda ake zargi da mallakar kuɗin jabun mai suna Ahmad Abdullahi.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, daga cikin waɗanda da ake zargin, sun shiga wani gida ne da nufin sata, inda har suka ga jabun kuɗaɗen a cikin wasu jakunkuna inda su kuma suka fara neman waɗanda za su canja mu su kuɗin zuwa Naira, wanda har ta kai ga aka kama su.

Kazalika, Abdullahi Kiyawa ya ƙara da cewa jabun kuɗin da aka kama za a dinga yin amfani da su wajen damfarar ƴan kasuwa ta hanyar shigar da su kasuwanni kaɗan-kaɗan.

Sannan ya ce da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da su a gaban kotu don su girbi abin da suka shuka.