Yan sandan Katsina sun ceto mutane 12 da aka yi yunƙurin safara zuwa Libiya

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta samu nasarar ceto mutane 12, waɗanda masu safarar mutane suka yi yunƙurin arcewa da su zuwa ƙasar Libiya.

Kakakin rundunar SP Gambo Isa ne ya bayyana hakan jiya a hedikwatar rundunar dake birnin Katsina.

A cewar Isa, masu safarar mutanen  sun yi yunƙurin tsallakawa da mutanen ne daga Nijeriya zuwa ƙasar Libiya ta hanyar amfani da iyakar Nijeriya da ƙasar Nijar.

Waɗanda aka ceto ɗin sun fito ne daga jihohin Kudancin ƙasar nan da suka haɗa da Kwara, Oyo, Edo, Osun da Ondo da kuma Ogun.

An ceto su ne a ranar Litinin, 2 ga watan Mayu na wannan shekarar da misalin ƙarfe 12:30 na rana a gidan wani mutum mai suna Yahaya Ɗahiru dake ƙauyen Kalgo na Ƙaramar Hukumar Daura dake jihar Katsina, biyo bayan wasu bayanan sirri da jami’an tsaron ‘yan sandan suka samu.

SP Isah ya ƙara da cewa tuni rundunar ta fara gudanar da bincike domin kamo mai gidan da aka sauke mutanen da kuma direban motar Mas’udu Dusha da ya ɗauko su, wanda ke zaune a ƙauyen ‘Yankara dake cikin Ƙaramar Hukumar Mai’aduwa.

Ya kuma ce za a miƙa mutanen da aka ceto ga Hukumar Yaƙi da Fataucin Bil’adama ta Ƙasa wato NAPTIP, domin ci gaba da bincike.

Ɗaya daga cikin su da ta zanta da manema labarai Adeleke Madinat, ta bayyana cewar za ta je Libiya ne don samun aikin yi, inda ta ƙara da cewa yayarta na can tana aikace-aikacen gidaje sai dai ta bayyana cewar ba ta san fita daga ƙasar nan ta haramtacciyar hanya laifi ne ba.

Shi ma wani Orobore Francis mai shekara 32 ya bayyana cewar matsin rayuwa da buƙatar iyali ya saka shi zai bar ƙasar nan don neman yadda zai rufa wa kansa asiri. Daga nan sai ya roƙi gwamnatoci da su samar wa ɗimbin matasan ƙasar nan aikin yi ko sun daina fita daga ƙasar ta haramtacciyar hanya.

Wannan nasarar na zuwa ne ƙasa da wata ɗaya bayan da Manhaja ta kawo labarin yadda ‘yan sanda a Katsina su ka ceto wasu mutane 15 daga hannun wasu masu safarar bil’adama waɗanda akasarinsu mata ne, bayan da jami’an tsaro suka tare motar da ta ɗauko su a Unguwar Baraje dake cikin Ƙaramar Hukumar Daura, inda ake ƙoƙarin yin safarar su zuwa ƙasashen Turai.

Mutanen dai sun fito ne daga jihohin Ogun, Ondo, Imo, Delta, Edo, Legas, Abiya da kuma Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja.