‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Haɗin gwiwa na jami’an tsaro a Jihar Katsina sun sami nasarar daƙile yunƙurin ‘yan ta’adda na kai mummunan hari a ƙauyen Ɗan Turaki da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa.
Hakan kuwa ya biyo bayan samun bayanan sirri da ofishin ‘yan sanda a yankin Ɗanmusa suka samu cewa ‘yan ta’addan sun yada zango a Dutsen Maijele a kan hanyar su na zuwa ƙauyen Ɗan Turaki domin kai hari.
Jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da haka a wata takardar sanarwar da ya rabawa manema labarai.
“Jami’an tsaron ƙarƙashin jagorancin DPO na ƙaramar hukumar suka afkawa ‘yan bindigan wanda nan take suka kashe mutum ɗaya wasu suka gudu ɗauke da manyan raunuka”inji DSP Abubakar.
Ya bayyana cewa jami’an tsaron sun sami bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya da tabar wiwi guda talatin da Adda guda ɗaya da kuma wasu miyagun ƙwayoyi da ‘yan bindiga suka bari a Dutsen.
CP Aliyu Abubakar Musa ya yaba da ƙwazo da ƙwarewa da jami’an tsaron suka nuna wajan tunkarar ‘yan ta’addan, sai ya yi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da baiwa jami’an goyon baya ta basu sahihin bayanan sirri domin tabbatar da tsaro a jihar.