‘Yan sandan sun tabbatar da kuɓutar da shugaban APC da aka yi garkuwa da shi a Neja

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja, ta tabbatar da kuɓutar da shugaban jam’iyyar APC na ‘Zone C’, Aminu Bobi, wanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi kwanan nan.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Wasiu Abiodun, shi ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Abiodun ya ce a ranar Juma’ar da ta gabata aka sami nasarar kuɓutar da Bobi da misalin ƙarfe 8:30 na dare, a dajin Igwama da ke yankin Bobi a ƙaramar hukumar Mariga da ke jihar.

Jami’in ya ce, bayan da aka kuɓutar da Bobi an kai shi Babbar Asibitin Kontagora don duba lafiyarsa. Tare da cewa, suna ci gaba da zurfafa bincike domin kamo waɗanda suka aikata ɗanyen aikin.

Kazalika, ya ce a ranar 7 ga Agusta waɗanda ake zargin ‘yan bindiga ne suka farmaki Bobi da direbansa a kan hanyarsu ta zuwa gona a hanyar Ukuru da ke yankin Bobi. Inda suka harbi direban a ƙafa suka bar shi a nan sannan suka yi gaba da Bobi.

Abiodun ya ce tun bayan faruwar lamarin ne aka haɗa wata runduna ta musamman da ta ƙunshi sojoji da ‘yan sanda da kuma bijilanti inda suka bazama bincike don gano maɓuyar ‘yan ta’addan.

Jami’in ya buƙaci jama’ar yankin da a taimaka wa jami’an tsaro da muhimman bayanai da za su taimaka wajen ceto ɗaliban makarantar Islamiyya ta Malam Salihu Tanko Tagina da aka yi garkuwa da su lokutan baya.