’Yan ta’adda sun fara ƙulafucin sababbin takardun Naira

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Bayan ƙaddamar da sababbin takardun kuɗi na Naira da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi, ’yan ta’addan sun buƙaci a fara ba su sababbin takardun kuɗin a matsayin kuɗin fansa kan sharaɗin sakin waɗanda suka kama.

Da ya ke jawabi a ranar Laraba a Abuja a wajen ƙaddamar da sabbin takardun kuɗi, gabanin taron majalisar zartarwa ta tarayya, Shugaban Ƙasar ya bayyana dalla-dalla dalilin da ya sa ya amince wa Babban Bankin Nijeriya (CBN) na sake fasalin kuɗin Naira 200, 500 da kuma 1000.

A halin da ake ciki, wasu ‘yan ta’adda a Jihar Zamfara sun yi garkuwa da mutane huɗu – namiji, mace, da yara biyu a ƙauyen Kolo da ke Ƙaramar Hukumar Gusau a jihar.

An tattaro bayanan cewa, masu laifin da suka buƙaci a biya su Naira miliyan 10 a matsayin kuɗin fansa, inda sun ƙi karɓar takardun Naira na yanzu, amma sun nemi a saki sabbin takardun kuɗin da aka sake fasalin a ranar 15 ga Disamba.

Wani mai suna Mohammed Ibrahim, ya yi iƙirarin cewa, a qarshe ’yan bindigar sun rage kuɗin da suka nema zuwa Naira miliyan biyar kuma mazauna unguwar sun yi ta ƙoƙarin tattara waɗannan kuɗaɗen.

“A yayin da muke ƙoƙarin tattara kuɗaɗen da ’yan ta’addan suka nema, sun sake aika da wani saƙo da safiya cewa ba za su karɓi tsoffin takardun Naira ba.

“Sun ce za su cigaba da ajiye waɗanda aka sace a sansanoninsu har sai an fitar da sabbin takardun Naira a Disamba,” inji Ibrahim.