Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane sama da 50 a ƙauyukan Jihar Zamfara, a yayin da mutanen suke aikin gona.
’Yan ta’addan sun kuma sanya wa mazauna ƙauyukan jihar harajin Naira miliyan 50 a kan ƙauye guda, da wa’adin mako biyu kacal.
Kazalika sun sanya tatar sama da Naira miliyan 100 a kan wasu ƙauyuka da ke ƙaramar Hukumar Tsafe, inda kowanne aka ayyana abin da mazaunansa za su biya, tskannain miliyan bakwai zuwa miliyan 20.
Hakan na zuwa ne bayan ’yan bindiga sun kashe manoma 10, suka sare kawunan shida daga cikinsu suka tafi da su a ƙauyukan Wayam da kuma Belu-Belu, da ke ƙaramar Hukumar Rafi a Jihar Neja.
Shaidu a Jihar Zamfara sun ce ’yan fashin daji a kan babura ne suka yi awon gaba da manoma sama da 50 a ƙauyukan ƙananan hukumomin Gusau da Gummi.
Wani mazaunin yankin ya ce “muna cikin damuwa, ba mu san halin da ’yan uwanmu ke ciki ba.
“Mutanen da aka sace sun kai aƙalla 50, ciki har da wani limami, wanda karo na biyu ke nan da aka sace shi. Har yanzu babu wanda ya tuntuɓe mu, balantana mu san halin da suke ciki. Maza bakwai ne a cikin waɗanda aka sacen, sauran mata ne da ƙananan yara.”
Ya ce ce, “maganar biyan kuɗin haraji ko tara kuma wannan ya zama duk shekara shekara bayan girbi, saboda sun san cewa manoma sun sayar da amfanin gona ko suna da shi a rumbuna, a takaice dai sun san cewa za a samu kuɗi a wurin manom,” in ji shi a hirarsa da kafar BBC.
An yi garkuwa da mutanen ne a yayin da suke tsaka da aiki a gonajinsi a yankin Wanke da kewaye, da ke kan hanyar Anka zuwa Gurusu a ƙaramar Hukumar Anka.
Wani mazaunin ƙauyen of Kwalfada, mai maƙwabtaka da Wanke, ya ce a gonaki daban-daban aka tusa ƙeyar manoman.
Ya ce fusatattun ’yan bibdigar sun yi barazanar harbe duk wanda ya yi yunƙurin tserewa.
Ya yi zargin ’yan ta’addan sun fusata ne a sakamakon tsananin ragargazar da sojoji ke musu a baya-bayan nan a jihar.
Ya ce, “Mun samu labarin cewa ’yan fashin dajin sun sanya wa ƙauyuka haraji, inda jagoran ’yan ta’adda Kachalla Halilu Sububu da Kachalla Mati, suka sanya wa harajin miliyan N50 a kan mazauna Kawaye cewa su biya cikin mako biyu ko a tashi ƙauyen gaba ɗaya.
“Shi kuma shugaban ’yan fashin daji Dan Yusuf, kanin shugabansu, Ado Alleiro ya sanya tarar sama da miliyan N100 wanda aka rarraba wa yankunan da ke Yammacin ƙaramar Hukumar, in ji shi.