‘Yan takarar ciyaman 38 sun faɗi gwajin auna fahimta a Kaduna

Daga UMAR M. GOMBE

Jam’iyyar APC ta jihar Kaduna ta bayyana rashin cancantar tsayawa takara na wasu mutum 38 daga cikin mutum 115 da suka nuna sha’awarsu ta tsayawa takarar shugabancin ƙananan hukumomin jihar.

Uwar jam’iyyar APC ta jihar ta ce, waɗanda lamarin ya shafa an same su da dalilan da suka hana canantarsu shiga takara kama daga dalili na mutum na da wani tabo na laifi da ya taɓa aikatawa ko kuma ya faɗi a gwajin auna fahimtar da aka ba su su rubuta.

Manhaja ta kalato cewa wannan shi ne karo na farko a tarihin Nijeriya da aka samu bai wa masu sha’awar takarar shugabancin ƙananan hukumomi gwaji a rubuce ya zama ɗaya daga cikin sharuɗdan da jam’iyya ke so a cika ga mai neman muƙamin ciyaman yayin zaɓen fidda gwani.

Baya ga wannan, sai da kuma ‘yan takarar, ɗaya bayan ɗaya suka fuskanci wani kwamiti mai mambobi 17 da suka haɗa da masana da ƙwararru domin amsa tambayoyi kan abin da suke sha’awar nema.

Binciken Manhaja ya gano cewa daga cikin tambayoyin da aka gabatar wa ‘yan takarar don su amsa su a rubuce, har da buƙatar mutum ya bada tarihin rayuwarsa, makarantun da ya halarta, sanin makamar aikinsa, inda yake da zama ko wuraren da ya taɓa ziyarta a ƙwaryar jihar Kaduna da ƙasa da ma ƙetare.

A cikin mutum 115 da suka sayi takardar nuna sha’awar tsayawa takara, an aminta da cancantar 75 daga ciki, yayin da 38 ba su cancanta ba sannan mutum 2 sun gagara dawowa da takardar balle ma a kai ga tantance su.

Da yake tsokaci game da sakamakon da aka fitar, shugaban APC na jihar Kaduna, Air Commodore Emmanuel Jekada (Rtd) ya ce, “Da ma ai ba kowannensu ba ne zai tsallake, manufar shirya jarabawar da aka ba su da kuma tantance su da aka yi, shi ne don bai wa kowa damar ya kare kansa.

“Mun ɗauki wannan mataki ne domin bambanta jiya da yau a sha’anin zaɓe, da kuma kimtsa jam’iyyar kafin zaɓen fidda gwani da kuma ainihin zaɓe.”

Uku daga cikin shugabannin ƙananan hukumomi masu ci na daga cikin waɗanda aka ce ba su cancanci tsayawa takara ba a shirin tantancewar da ya gudana, wato shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta tsakiya da sauransu.