‘Yan wasa 8000 ne za su fafata a bikin wansannin motsa jiki na Edo – Minista

Daga UMAR M. GOMBE

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbaccin za a gudanar da bikin wasannin motsa jiki da aka shirya gudanarwa a jihar Edo kamar yadda aka tsara. Ministan Harkokin Matasa da Wasannin Motsa Jiki, Chief Sunday Dare ne ya bada wannan tabbaci a garin Benin, Juma’ar da ta gabata.

A cewar Dare, bikin wanda ake sa ran ya ƙunshi ‘yan wasa 8000, zai gudana ne daga ranar 2 zuwa 4 ga Afrilun 2021.

Da yake jawabi bayan kammala zagayen duba kayayyakin wasa da kuma ganawa da gwamnan jihar, Godwin Obaseki, Ministan ya ce, “za a buɗe sansanin ‘yan wasa na bikin a ranar 2 ga Afrilu mai zuwa, sannan a buɗe bikin a hakumance, Afrilu, 6 ga wata, wanda Shugaban Ƙasa zai jagoranta.

“Muna aiki kafaɗa da kafaɗa tare da hukumomin PTF da NCDC da sauransu domin samun gudunmuwar allurar rigakafin da za a yi wa ‘yan wasa da sauran kayan aiki.

“Sannan mun rage yawan ‘yan wasa daga 14,000 zuwa 8,000. Ya zama wajibi in nuna godiyata ga gwamnan jihar da kuma mataimakinsa bisa ƙoƙarin da suke yi wajen ganin wannan biki ya gudana cikin nasara.”

Ta ɓangaren abin da ya shafi masaukin baƙi kuwa, Ministan ya ce sun dace da samun Jami’ar Benin a matsayin wurin da za a sauki ‘yan wasa. Ya ci gaba da cewa duk da dai akwai sauran ‘yan shirye-shirye da ba a kammala ba, amma cewa komai na tafiya daidai.

Idan dai za a iya tunawa tun a bara aka shirya gudanar da bikin amma sai aka ɗaga saboda dalilai na annobar korona.