Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Katin gargaɗi wato ‘Yellow Card’ kati ne wanda alƙalin wasa yake bawa ɗan wasa domin ya rage duka da sauran wasu ɗabi’u da basu kamata ba yayin da ake fafata wasa a tsakiyar fili.
Akwai wasu ’yan wasa guda biyar da tarihin katin gargaɗi bazai taɓa mantawa da su ba har kawowa iyanzu.
Ga jerin sunayen ’yan wasan da suka fi ɗaukar katin tun daga na 1 har zuwa na 5.
Sergio Ramos:
Sergio Ramos Garcia ɗan wasan ƙasar Sifaniya wanda yake fafata wasan sa a Paris saint-german da tawagar ƙasar Spain. Yana doka wasan sa ne a vangaren tsakiya na baya, inda ya kwashe kakar wasa 16 yana takawa Real Madrid leda kafin ya koma PSG. Ya samu katin gargaɗi a rayuwar sa ta ƙwallon ƙafa guda 259 tare da Jan kati guda 26.
Gerrado Terrado:
Gerardo Torrado Diez de Bonilla ɗan wasan ƙasar Mexico shine na biyu a cikin waɗanda suka fi samun katin gargaɗi a duniyar qwallon ƙafa da guda 228.
Dani Alves:
Dani Alves da Silva ɗan wasan ƙasar Brazil wanda yake fafata wasan sa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da ke fafatawa a gasar La Liga. Shine ɗan wasa na uku da yafi kowa ɗaukar katin gargaɗi a duniyar qwallon ƙafa da guda 210.
Xabi Alonso:
Xabier Alonso Olano ɗan wasan ƙasar Sifaniya wanda ya yi wasa a Real Madrid da Bayern Munich kafin yayi Ritaya. Ya samu katin gargaɗi sau 197 a ƙwallon ƙafa.
Gabi:
Gabriel Fernandez Arenas wanda aka fi sani da Gabi tsohon ɗan wasan ƙasar Sifaniya da Atletico Madrid wanda yake fafata wasan sa a gurbin tsakiya. Ya samu katin gargaɗi sau 189 kafin ya yi Ritaya a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.