Yanayin kare haƙƙin ɗan Adam na ‘yan ƙananan ƙabilun Sin ya kai matsayin ƙoli a tarihi

Daga CMG HAUSA

Mataimakin darektan huhumar kula da harkokin ƙabilun ƙasar Sin Zhao Yong, ya ce ƙasar Sin ta samu sabon sakamako a tarihi, yayin gudanar da aikin hada kan ƙabilu daban daban na ƙasar, kuma yanayin kare haƙƙin ɗan adam na ‘yan ƙananan ƙabilun Sin ya kai matsayin ƙoli a tarihi.

Jami’in ya bayyana hakan ne a Larabar nan, yana mai cewa, idan an waiwayi tarihin JKS cikin tsawon shekaru 100, za a lura cewa, babban sakamakon da aka samu a aikin haɗa kan ƙabilun ƙasar, shi ne an samu wata hanyar daidaita matsalar ƙabilu mai tsarin musamman na ƙasar Sin, wato dukkannin ƙabilun ƙasar suna zaman jituwa bisa tushen daidai wa daida.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa