Daga LAWAL SALE
Sufuri dai abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar dan adam ta fannin zirga-zirga da dakon kaya daga wannan wuri zuwa wancan.
Kafin zuwan zamanin kekuna, da motoci da layin dogo da jiragen sama, ana amfani ne da dabbobi kamar raƙuma da dawakai da jakuna domin tafiye-tafiye da dakon kaya na yau da kullum.
A wancan lokacin, ƙasar Sin da ƙasashe da dama sun yi amfani da irin wannan nau’in sufurin a zirga-zirgar da aka fi sani da “silk road’’ wato hanyar siliki domin kasuwanci tsakaninsu.
Daga nan dai aka fara samun ci gaba a yayin da kekuna suka ɓullo da motoci da sauran ababen hawa.
A yau kamar yadda kowa ya sani, ƙasar Sin tana kan gaba a sufuri na zamani, kamar irin su layin dogo mai sauri da motoci masu amfani da sabbin makamashi da jiragen sama da filayen jiragen sama na zamani da dai sauransu.
Kamar yadda na lura a ziyarar da na kai a ƙasar a lokuta daban-daban, na fahimta cewa ana ba layin dogo ko kuma jirgin ƙasa muhimmanci a Sin, a yayin da akwai nau’in layin dogo iri-iri, wanda suka haɗa da layin dogo mafi sauri wato HSR (ko kuma bullet train) wanda ke da saurin tafiya na kilomita 200-350, da layin dogo na ƙarƙashin ƙasa (metro).
Masana sun nuna cewa a duk faɗin duniya, layin dogo shine hanya mafi sauƙi domin zirga-zirga da dakon kaya.
Jama’a da dama dai suna amfani da layin dogo a ƙasar Sin.
Akwai dai burgewa da ban sha’awa a yayin da na yi amfani da waɗannan nau’in layukan dogon yayin da na je larduna da garuruwa a cikinsa, kamar daga Beijing zuwa Shanghai, da Beijing zuwa Nanjing, da Xi’an zuwa Chengdu da dai sauransu.
A duk wannan lokutan, tafiyar tana mai matuƙar nishadi wanda mutum zai ji kamar yana cikin jirgin sama ne, domin kuwa kirar wannan jirgin kasan tamkar irin na jirgin sama ne, ana dai shafe misalin awa 4 ne kacal a tafiyar kilomita 1,302. An dai ƙiyasta jimlar tsawon layin dogo gaba ɗaya a ƙasar Sin a akan kilomita sama da dubu 150 wanda kuma shi ne mafi tsawo a duniya.
Kamar yadda na ambata, layin dogo na ƙarƙashin ƙasa (metro) ko kuma (subway) akwai shi kusan a duk faɗin larduna ƙasar Sin, jirgin ƙasa ne mai ƙayatarwa da ban mamaki ga wanda ya fara ganinsa ko amfani da shi.
Wannan layin dogon dai yana kama da sauran layukan dogo na zamani amma a can cikin ƙarƙashin ƙasa layinsa da tasoshinsa suke.
Ana dai amfani da shi ne a zirga-zirga a cikin gari da kewaye.
A misali a babban birnin Bejing, yayin da na ziyaci birnin, a ko da wane lokaci zan leƙa shaguna ko wurin shaƙatawa ina amfani da shi, domin yana da sauri da arhar tikiti da biyan buƙata a cikin lokaci.
A fannin sufurin jiragen sama, ƙasar Sin ma ba’a bar ta a baya ba, domin kuwa akwai dimbin kamfanonin jiragen sama na fasinja da dama, da kuma filayen jiragen sama na zamani a kowane lardi.
Aƙalla akwai tasoshin jiragen sama kamar 370 a duk faɗin ƙasar.
A cikin tasoshin jiragen sama akwai manya guda biyu a Beijing, wato tashar jiragen sama ta ƙasa da ƙasa da kuma Beijing Daxing.
Daxing dai sabuwa ce wacce aka gina shekaru uku da suka wuce kuma tafi ko wace tashar jirgin sama girma a duniya, tashar jiragen sama ta zamani ce kuma tana da kyau matuƙa.
Akwai motocin hawa masu amfani da sabbin makamashi a ƙasar Sin ma, kuma ƙasar na gaba a kan tabbatar da an rage amfani da motoci masu tafiya da man fetur ko disel domin kare muhalli don kyautata lafiyar jama’a.
Abin da ya ba ni sha’awa shine irin wadannan motoci suna da lambar lasisi ta musamman, domin duk mota mai amfani da sabbin makamashi kalar lambarta kore ce.
A sakamakon irin wannan ci gaba a fannin sufuri da ƙasar Sin ta samu kuma ta zama a gaba a duniya, ya sanya Sin tana taimaka ma nahiyar Afirka da ƙasashe masu tasowa kafa ire-iren wadannan ababen more rayuwa ta hanyar haɗin gwiwa.
A misali, a Najeriya, a ƙarƙashin haɗin gwiwa da ƙasar Sin, an samu gina hanyoyin layin dogo, da tasoshin jiragen sama da hanyoyin mota da tasoshin jiragen ruwa.
Waɗannan ababen more rayuwa ta fannin sufuri dai suna da muhimmanci a rayuwar dan adam da ci gaban tattalin arzikin ko wace ƙasa.