‘Yancin Zaɓi

Daga AMINA HASSAN ABDULSALAM

Kwanaki na haɗu da wata uwa wace ɗanta ya sami gurbin karatun injiniya a jami’a, bayan ya biya kuɗin na gani na karɓa, wato acceptance fee sai aka ce masa ai ya yi kuskuren haɗin gambiza a jarabawar samin gurbin karatun jami’a wato jamb ko UME ɗin sa don haka an janye gurbin karatu da aka ba shi. Iyayen yaron ganin yadda yake da ƙwazo suka yi duk yadda za su yi yaron ya karanta abinda ransa ke muradi abin ya faskara, a ƙarshen sai wani kwas ɗin aka ba shi wanda bai kai na injiyan daraja ba. Tun daga lokacin yaron ya sauya hali kamar ba shi ba saboda baqin cikin rasa abinda yake burin karantawa a jami’a.

Hakazalika yaran da aiyayensu ke tilasta wa ɗaukar fannin da ba shi suke da burin karantawa ba ke shiga halin damuwa domin an takura musu da abinda zai zame musu takura a rayuwa. Misali akwai yaran da suke da basira da hikima da fasaha a wasu fannonin da ba na fasaha da kimiyya ba, sai iyayensu su tursasa su su zaɓi ajin kimkiyya, sai tafiya ta yi tafiya an gama ɓata lokaci an gama kashe kuɗi sai matsala ta auku, su ga cewa yaron ma ba karatu yake ba saboda ba zaɓin sa ba ne. Labarin can na sama ya nuna cewa yaro bai sami zaɓinsa ba shi ya sa ya shiga damuwa bare kuma ƙiri-ƙiri yaro yana gani za a tursasa shi ya yi abinda kwata-kwata ba ya so.

Da yawa iyaye su kan yi watsi da yaran da suke da basira ta musamman kamar ta rubutu ko waƙa ko zane ko iya sarrafa wata sana’a ta hannu, a ganinsu duk daƙiƙanci ne ke kawo haka sannan kuma yaron ba zai sami cigaban rayuwa ba saboda ya zaɓi abinda ba zai yi suna ko kasuwa ba. Iyaye sun fi son su ji ‘ya’yansu su ce za su yi karatun zama lauya ko likita ko injiniya da sauransu, to annan farin cikinsu zai bayyana. Wasu iyayen ma ba sa qaunar su ji yaransu su ce za su karanci fannin da suke ganin yana da ƙarancin farin jini a kasuwar ƙwadago ko karatun da al’umma ba ta ganin darajarsa sosai.

Idan muka duba abubuwan da suke faruwa dangane da zaɓin abinda yaro zai karanta ko irin aikin da yaro zai yi, wato profession kenan a turance, za mu ga cewa al’umma irin tamu tana yi wa sana’ar wala kallon aiki ne na ‘ya’yan talakawa ko marasa galihu ko mara mafaɗi, sannan hanya ce ta ɓatattun mutane, ko kuma ka ji ana cewa hanya ce ta Yahudawa don a vatar da mutum. Babban abinda za a duba shi ne waƙa ta kasu kashi-kashi sai a duba wace za ta dace da mutum da rayuwarsa. Akwai waƙar baka akwai rubutacciya da kuma mai kiɗa dukkansu na kai mutum ga ɗaukaka, abin dubawa shine kada mutum ya yi wace zai iskance.

A ɓangaren zane-zane kuma da yawan mutane kan ɗauka cewa malalacin yaro ko mara ƙoƙari ko daƙiƙi ke tsunduma harkar zane domin suna ganin ba shi da ƙwaƙƙwarar hanyar cin abinci, nan da nan sai iyaye su sauya masa ko su zaɓa masa wani abin daban. Ko karatun fannin lafiya aka zaɓa wa yaro bisa dole, zai yi ne ba da daɗin rai ba, idan ya sami matsala nan gaba a yayin aikin nasa zai zargi waɗan da suka ƙaƙaba masa yin karatun tun asali sannan irin waɗan nan yara ko ma’aikatan da za su zama nan gaba ba su cika ba da kyakkyawar kulawa ga mara lafiyar da suka gamu da su ba a yayin rayuwar aikinsu.

Akwai iyayen da suke wa ‘ya’yansu duka irin na jaki domin yaran sun fi mayar da hankulansu ga buga ƙwallon ƙafa, su a ganin su rashin mayar da hankali ne ga karatu ko da kuwa yaron yana taɓuka abin arziƙi a makaranta, wannan ba zai sa su ba shi goyan baya ga burinsa na son zama qwararre ko shahararren ɗan ƙwallo ba. Har akan sami iyaye da suke daƙile ƙoƙarin yaransu da suke burin zama marubuta. Sun manta cewa waɗan nan abubuwa baiwa ce ta musamman da Allah Yake ba wa wasu, ba kowa bane yake iya yinsu duk ƙaunarsu da su.

Har yanzu al’ummar Hausawa suna tare da ɓurɓushin ƙin jinin sana’ar fim, har yanzu a wajensu sana’a ce ta ‘yan iska ta mara sa tarbiyya, wannan kuma ya danganta da yadda shi ɗan fim ɗin yake, in mutumin kirki ne hakan za a ganshi in na banza ne hakan za a gan shi, kowacce sana’a tana da baragurbi da kuma na arziƙi. Duk da haka hankalin mutane bai ga